18 Afirilu 2025 - 17:36
Sakamako Mafi Muni A Ta'addancin Kisan Kiyashin Isra'ila A Gaza Bayan Kwanaki 560

Ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya wallafa a yau Juma'a, wani cikakken kididdiga kan mafi girman sakamakon yakin kisan kare dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi a zirin Gaza, kwanaki 560 bayan fara kai hare-hare daga ranar 7 ga Oktoba, 2023 zuwa 18 ga Afrilu, 2025.

Sanarwar da ofishin ya fitar a yau Juma’a ta ce adadin kisan kiyashin da ‘yan mamaya suka yi ya zarce dubu 12, wanda ya yi sanadin samuwar shahidai da bacewar mutane sama da 62,000, ciki har da shahidai 51,065 da gawarwakinsu ya isa asibitoci, yayin da wasu sama da 11,000 suka bace, ciki har da wadanda suka mutu a karkashin baraguzan ginin, ko kuma ba a san makomarsu ba.

Sanarwar ta yi nuni da cewa, mamayar ta aiwatar da kisan kiyashi 11,859 kan iyalan Palasdinawa, wanda ya yi sanadin kawar da iyalai 2,172 gaba daya tare da shafe su daga rajistar farar hula yan ƙasa, tare da shahadantar da dukkan mambobinsu. Fiye da iyalai 5,070 kuma an share su, yayin da mutum ɗaya kawai ya tsira daga cikin iyalan.

Alkaluma sun nuna shahadar kananan yara sama da 18,000 da suka hada da yara 281 da aka haifa a lokacin yakin, yara 892 da suka mutu kafin cikar su shekara ta farko, 52 kuma sun mutu sakamakon yunwa, sannan 17 kuma suka mutu sakamakon sanyi, yawancinsu kananan yara ne.

Sama da mata 12,400 ne suka yi shahada, sannan jami’an kiwon lafiya 1,402, jami’an tsaron farin kaya 113, ‘yan jarida 211, da ‘yan sanda da jami’an agaji 748 ne sojojin mamaya suka kai musu hari kai tsaye.

Ofishin yada labaran ya bayyana kasancewar wasu manyan kaburbura guda bakwai a cikin asibitoci, inda aka gano gawarwaki 529. Rahoton ya kuma rubuta adadi 116,505 da suka samu raunuka, ciki har da 17,000 da ke bukatar gyara na dogon lokaci, da kuma yanke sassa 4,700, 18% daga cikinsu yara ne.

Sanarwar ta bayyana cewa kashi 60 cikin 100 na wadanda abin ya shafa mata ne da kananan yara, sannan 409 'yan jarida ne suka jikkata a lokacin yakin. An kai hari kan gidaje 232 tare da kama mutane 6,633 daga Gaza, ciki har da ma'aikatan lafiya 362 da 'yan jarida 48.

Dangane da lalatawa da rushe gidaje kuwa, ofishin ya kiyasta lalata yankin na Gaza da fiye da kashi 88%, tare da rusa gidaje 165,000 gaba daya, sama da 300,000 sun lalace. Asarar tattalin arzikin farko ta kai sama da dala biliyan 42.

Ya kara da cewa dakarun mamaya sun lalata masallatai 828 gaba daya, sannan sun lalata ɓangaren wasu 167, sun kai hari kan majami'u uku, wani bangare ko kuma gaba daya sun lalata makabartu 19, tare da sace gawarwaki 2,300.

Asibitoci 38 da cibiyoyin kiwon lafiya 81 sun daina aiki, sun kai hare-hare kan cibiyoyin lafiya 164 da motocin daukar marasa lafiya 144, an lalata rijiyoyin ruwa 719, an lalata dubban kilomita na titina, hanyar ruwa, da hanyoyin wutar lantarki.

A fagen ilimi kuma dalibai 13,000 ne suka yi shahada, 785,000 kuma aka hana su karatu, an kuma kai hari ga ma’aikatan koyarwa 800 da malaman jami’o’i sama da 150, an kuma lalata cibiyoyin ilimi 142 gaba daya sannan 364 an lalata bangarensu.

Yara 39,400 ne ke rayuwa ba tare da daya ko duka biyu ba na iyayansa ba, kuma iyalai 280,000 sun rasa matsuguni, ba su samu taimakon jin kai da na likitanci sakamakon kawanya da kuma lalata tsari.

Ofishin yada labaran ya kammala bayaninsa da jaddada cewa, wadannan alkaluma sun nuna girman laifukan da ake ci gaba da aikatawa a zirin Gaza, a daidai lokacin da kasashen duniya sukai shiru. Ta kuma yi kira da a dauki matakin gaggawa don dakatar da kai hare-hare tare da dage wa al'ummar Falasɗinu kawanyar da ake masu.

Your Comment

You are replying to: .
captcha